By Abbas Yakubu Yaura
Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu, Nora Dadu’ut, da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Wase a majalisar wakilai, Idris Wase, sun yi Allah wadai da harin da aka kai kauyen Pinau dake karamar hukumar Wase ta jihar Filato.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a ranar Lahadi sun kai hari a yankin Pinau, inda suka kashe mutane kusan 10 yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban.
‘Yan majalisar dokokin kasar, a jawabansu daban-daban a ranar Litinin, sun yi tir da harin tare da yin kira ga jami’an tsaro dasu tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Dadu’ut yace kamata ya yi a sanya maharan su biya kudaden da suka lalata tare da bayyana ci gaban da aka samu a matsayin abin takaici duk da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.
“Ina kira ga jami’an tsaro da su bi wadanda ke kai farmaki ga mutanen kauyukan da ba su ji ba ba su gani ba, don haka a sanya su su biya kudin wannan danyen aikin da suka aikata,” in ji dan majalisar.
Rahotanni sun bayyana cewa harin da aka kai a yankin Pinau ya faru ne jim kadan bayan mutanen kauyen sun rufe kasuwarsu dake yankin.
Wani shugaban matasa a yankin, Nantip Padur, wanda ya tabbatar wa da jaridar PUNCH a Jos kisan gilla a ranar Litinin din da ta gabata ya ce an kuma jikkata wasu da dama yayin harin.
Padur yace, “Ina iya tabbatar muku da cewa an kashe mutanenmu kusan 10 bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Pinau. Maharan sun kuma jikkata wasu da dama.”Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadi yayin da kasuwar garin take ci.”
Ya ce kafin sabon harin ‘yan bindigar sun kai hari garin Sapiyo inda suka yi garkuwa da wata mata mai shayarwa da wani fitaccen dan siyasa.