-Hukumar Hisba ta Jihar Kano
Hukumar Hisba ta Jihar Kano, da reshenta na karamar Hukumar Nassaraw a cikin garin Kanon, ta bayyana cewa ta fahimci cewa, ýam matan jihohin Yobe, Borno, da Adamawa ke shigowa cikin Kano suna lalata tarbiyar ýaýan kanawa.
A cikin shirin INDA RANKA na daren yau na Gidan Rediyon Freedom Rediyo da ke Kanon na Dabo, sun kawo hirar da su ka yi da daya daga cikin Jamián Hisba mai suna Idris Bin Umar, wanda ya furta haka.
Ibn Umar ya cigaba da cewa tsananin talauci, auren dole, rashin zaman lafiya da son shiga cikin fina-finan Hausa ya sanya irin wadannan ýam mata kan bijiro cikin Kano domin neman yadda za su sami rufin asirin rayuwa.
Daga nan gidan Rediyon ya kawo hirar da ya yi da wata (Mun boye sunanta), wadda ta ce ta gudo ne daga jihar Borno take fantamawa a garin Kano saboda auren dole da aka yi mata.
HISBA NASSARAWA.
Haka nan, gidan Rediyon ya bada labarin wata budurwa wadda su ka ce daga jihar Kaduna ta zo ta yi zaman dirshan a Kano, wadda take koya wa ýaýan kanawan muguwar dabiár nan ta MADIGO.
A hirar da gidan rediyon ya yi da ita, yarinyar wadda aka sako muryarta, amma ba a tambaye ta sunanta ba, ta ce ita abin da Hukumar Hisbar ta fada ba gaskiya ba ne. Ta ce Hisba sun afka cikin gidan da su ke ne, suka kamo su, amma ita ba ta koya wa kowace yarinya MADIGO.
”Yanzu ina tambayar Hisba. Da su ka shiga su ka kamo mu, sun kama mu muna yin MADIGO ne? Kuma yanzu kai idan aka shigo dakinka ba tare da izini ba, idan aka sameka babu riga a jikinka, yana nufin kana yin wani abu maras kyau ne”. In ji wannan yarinyar.
Hukumar Hisba dai ta ce za ta gabatar da su a gaban Shariá.