Akalla ‘yan Najeriya 126 da suka makale a kasar Sudan sun isa Abuja ranar Asabar sakamakon ci gaba da rikicin kasar da yaki ya daidaita.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa mutanen da suka dawo sun iso ne a cikin wani jirgin saman Tarco Aircraft ST-TAL B737-300 da misalin karfe 5:15 na yamma.
KARANTA WANNAN: Jerin Jami’o’in da Suka Amince da 200 a Matsayin Mafi Karancin Maki
Ma’aikatan NEMA, Ma’aikatar Harkokin Waje, Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Kasa, NIDCOM, NAPTIP, da sauran su ne suka tarbi mutanen da suka dawo.
Majiyar mu ta kuma rawaito cewa daga cikin mutane 126 da aka kwaso uku dalibai ne yayin da 23 yara ne.
Wannan ya kawo adadin ‘yan Najeriya 2,660 da suka makale da aka kwaso zuwa kasar cikin rukuni 16 tun bayan barkewar rikicin a Sudan.
An bai wa wadanda aka dawo da su kudi Naira 100,000 da kuma abinci da abin sha da isar su.
Mista Mustapha Ahmed, Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA ya yi maraba da wadanda suka dawo a madadin gwamnatin tarayya.
Ahmed wanda ya samu wakilcin Dr Onimode Bandele, Daraktan ayyuka na musamman na hukumar NEMA, ya ce an yi shirin dawo da wasu ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan.
“Wannan kwashen ya fara ne tun kafin karshen gwamnatin da ta shude, kuma kasancewar gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta gaji wannan tsari kuma ya ba mu goyon bayan da ya kamata mu dawo da su.
“Nasarar da muke gani a yau ita ce, gwamnatin tarayya ta tallafa mana, kuma babban daraktan hukumar NEMA ya jajirce wajen ganin an fitar da wadannan jirage daga Port Sudan.
Mista Akwari Henry, wanda ya ke zaune a kasar Sudan tsawon shekaru shida, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa dawo da su kasar.
“Ina buga kwallon kafa a wata kungiya a Sudan kuma na shafe shekaru shida a can. Ba na addu’ar mu fuskanci irin wannan rikici a Najeriya saboda abin da ya faru ya kasance mai ban tsoro.
“Ina fatan kungiyoyin kwallon kafa a Najeriya za su gayyace ni don in fara rayuwa,” in ji shi.
Ita ma wata ‘yar kasar da ta dawo, Misis Bilqis Bamijoko, ta kuma yabawa gwamnatin tarayya da ta dawo da su kasar.
“Tun daga watan Afrilu lokacin da aka fara yakin, ba mu iya yin barci ba saboda yin maganar cin abinci mai kyau amma ina farin cikin dawowa gida,” in ji ta.
Majiyar mu ta rahoto cewa, an fara rikici tsakanin bangarorin da ke adawa da gwamnatin mulkin sojan kasar Sudan a ranar 15 ga watan Afrilu, lokacin da rikici ya barke a garuruwan da ke yankunan Khatourm da Dafur.
A wani labarin kuma, Ba Mu Taba Gayyatar Wike Ya Koma Cikin Jam’iyyarmu Ba – APC
Jam’iyyar APC reshen jihar Rivers ta musanta cewa ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike zuwa cikin jam’iyyar
APC ta bayyana wadanda ke ikirarin neman Wike ya koma jam’iyyarsu a matsayin masu yin zagon kasa
APC ta ce Wike ya ji kunyar shiga jam’iyyar da ya bayyana a matsayin ciwon daji