Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta ce kimanin ‘yan Najeriya 159 ne suka yi watsi da zama ‘yan kasa a shekarar 2022 kadai.
Babban sakataren ma’aikatar Dr Shu’aib Belgore ne ya bayyana haka a taron ministocin majalisar dokokin kasar karo na 64 da kungiyar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya, a fadar shugaban kasa dake Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Obasanjo Da Fayemi Sun Gana Da Wike A Jihar Rivers
Kafin kuma a ce ‘yan Najeriya 150 sun yi watsi da zama ‘yan kasa tsakanin shekarar 2006 zuwa 2021.
A cikin shekarar 2022, duk da haka, ‘yan Najeriya 159 suka yi watsi da zama ‘yan kasa.
A halin da ake ciki, Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya ce yawan kaura da ‘yan Najeriya ke yi daga yankin domin neman wuraren kiwo ne ya jawo yawaitar kwararowar mutane masu neman fasfo.
Ministan ya ce a shekarar 2022, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, NIS, ta fitar da mafi girman adadin fasfo din da ya kai 1,899,683 cikin sama da shekaru bakwai.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Gbajabiamila Ya Yi Barazanar Kama Emefiele Kan Wa’adin Tsoffin Kudin Naira
Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa a shirye ya ke ya bayar da sammacin kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele idan har ya ki gurfana a gaban kwamitin ta ranar Alhamis.
Gbajabiamila ya ce a maimakon majalisar ta dage zaman har zuwa ranar 28 ga watan Fabrairu domin gudanar da zabukan kamar yadda aka tsara, ‘yan majalisar za su sake zama ranar Talata domin daukar mataki kan Emefiele da sauran shugabannin bankunan da suka kasa halarta.