Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi sun gana da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers, ranar Alhamis.
Obasanjo da Fayemi sun halarci taron kasa da kasa na Fatakwal 2023 da ke gudana a dakin taro na Obi Wali International Conference Centre, Fatakwal.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Gbajabiamila Ya Yi Barazanar Kama Emefiele Kan Wa’adin Tsoffin Kudin Naira
An yi wa taron lakabin, “Zurfafa Al’adu da Cibiyoyin Dimokuradiyya don Ci gaba da Tsaro a Najeriya.”
A wani labarin kuma, Wata Mata Ta Fada Komar Jami’an Tsaro Bisa Lakadawa Danta Duka Har Lahira Kan Batan Naman Miya
Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe ta tabbatar da cafke wata uwar ‘ya’ya biyu mai suna Misis Charity Upev bisa zarginta da lakada wa yaronta mai suna Fanen dan shekara 10 da haihuwa duka inda ta kashe shi har lahira sakamakon wani nama da ya bata.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 23 ga watan Janairu, 2023, a kan titin Abu King Shuluwa, kusa da kasuwar duniya, bayan Deeper life camp a Makurdi, babban birnin jihar.
An tattaro cewa an kama wadda ake zargin ne bayan da makwabtanta suka kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda ‘E Division’ dake jihar.
Wata majiya a unguwar da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa mutuwar marigayin kusan ta haifar da zanga-zangar fusata da matasan yankin da suka so nuna fushinsu a kan wanda ake zargin amma jami’an ‘yan sanda sun yi gaggawar shiga cikin lamarin.
Majiyar ta shaida wa Jaridar Vanguard cewa, “An ce matar ta yi wa yaron dukan tsiya da safiyar ranar Lahadi bisa zarginsa da dauke wani nama a cikin tukunyar miyar ta, amma da yamma sai yaron ya fara amai da abin da ake zargin jini ne.
“An garzaya da shi Asibiti, jim kadan bayan rasuwarsa, don haka kowa na cewa yaron da ke a gidan matar, tabbas ya samu zubar jini a ciki wanda ya kai ga mutuwarsa.
“Duk da cewa wannan hasashe ne saboda har yanzu ba a gama binciken gawar ba kan abin da ya yi sanadin mutuwar ba, amma abin da ake dauka a unguwar shi ne ya mutu ne sakamakon duka da aka yi masa a safiyar ranar.”