Rahoton Bankin Duniya na shekarar 2022 ya nuna cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 70 ne ba su da hanyoyin samun ruwan sha sannan miliyan 114 ba su da wuraren tsaftar muhalli a shekarar 2021.
Rahoton mai suna, ‘Global Water Security & Sanitation Partnership’ ya nuna cewa samun ruwan famfo ya ragu daga kashi 36 cikin 100 a shekarar 1990 zuwa kashi 11 cikin 100 a shekarar 2021.
KARANTA ANAN: Gwamnatin Tarayya Ta Musanta ‘Daukar Ma’aikata
Rahoton ya kara da cewa, “A shekarar 2021, kimanin ‘yan Najeriya miliyan 70 ne ba su da hanyoyin samar da ruwan sha sannan miliyan 114 ba su da kayan tsaftar muhalli. Samun ruwan famfo ya ragu daga kashi 36 cikin 100 a shekarar 1990 zuwa kashi 11 cikin 100 a shekarar 2021. Kimanin kashi 19 cikin 100 na ‘yan Najeriya suna yin bahaya a fili a shekarar 2020, kuma ana fitar da najasar ba tare da kula da muhalli ba.
“Kamfanonin ruwa na birni sun kasa biyan bukatun abokan cinikinsu da suka riga sun kasance, wanda hakan ke tilastawa yawancin su dogara ga kayayyaki masu tsada kuma galibi marasa aminci, kamar masu sayar da ruwa masu zaman kansu da rijiyoyi masu zaman kansu.
“A cikin shekarar 2016, gwajin ingancin ruwa a ma’aunin ƙasa ya nuna cewa sama da kashi uku cikin huɗu na yawan jama’a sun yi amfani da gurɓatattun hanyoyin samun ruwa, kuma kusan rabin su sun yi amfani da hanyoyin da ke cikin haɗarin gurɓatawar najasa.”
Rahoton, duk da haka, ya nuna cewa GWSP ya ba da taimako mai mahimmanci don tallafawa kudurin gwamnati na yin gyare-gyare da kuma inganta karfin gwamnati.
Da yake tsokaci kan rahoton, Farfesa Tanimola Akande, Farfesa a fannin kiwon lafiyar al’umma, ya ce abin takaici ne yadda samun tsaftataccen ruwan sha babban kalubale ne a Najeriya.
“Samar da ruwan sha na yau da kullun yana nufin samun ruwa daga ingantacciyar hanyar da ake samu a gida, ana samunsa idan an buƙata, kuma ba tare daya gurɓata da najasa da sinadarai ba.
“Rashin samun tsaftataccen ruwan sha yana haifar da cututtuka da dama, musamman cututtukan gudawa. Nauyin wadannan cututtuka ya yi yawa a Najeriya. Har ila yau, tana da alhakin mutuwar adadi mai yawa.
“Don inganta yanayin kowa yana da rawar da zai taka. A matakin gida, ya kamata mutane su yi kokarin samun ruwa ta hanyoyin ruwa daban-daban da kuma kula da ruwan a gida don kare lafiyarsu,” in ji Akande.
A wani labarin kuma, Da Alama Qatar Za Ta Maimaita Tarihin Abinda Ya Faru Shekaru 12 Da Suka Gabata
Wani mai sharhi kan harkokin wasanni a jihar Kano Abdulkarim Abdullahi Tsoho ya ce da alama Qatar a gasar cin kofin duniya ba za ta kai labari ba.
Abdulkarim Tsoho yayin ganawarsa da Dimokuradiyya ya ce makamancin hakan ya faranta faruwa da kasar Afrika ta Kudu a shekarar 2010.