Jami’an Rundunar Yan Sandar Jihar Ogun sun yi nasarar Kubutar da Mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a hanyar Siun zuwa Ajura dakw ƙaramar hukumar Obafemi-Owode ta Jihar.
Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar DSP Abimbola Oyeyemi shi ya tabbatar da wannan nasara wa manema labarai a yau juma’a, inda ya ce Motar mutanen ta Kakarw ne a bakin hanya wuraren karfe uku dare nan ne fa yan bindigar suka samu Nasarar hankada keyar su zuwa daji yayin da sauran Fasinjoji Kuma ALLAH Ya musu gyadar dogo.
DSP Abimbola ya ce bayan jin labarin aukuwar lamarin ne Kwamishinan Yan Sandar Jihar Edward Ajogun ya umarci Kwamandar Rundunonin yanki da ya tura jami’an shi su bazama dajin da ake zargin an yi garkuwa da mutane.