Rundunar Yan Sandar Jihar Enugu ta chafke wata mata mai shekara 29 da laifin Kashe dan kishiyar ta mai suna Wisdim Egwuagu ta hanyar sanya mishi guba.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta labarto cewa wannan guba da ta tafka ma yaron ita ce dai ta yi silar shi ta bankwana da duniya.
Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar ta Enugu ASP Daniel Ndukwe ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar tara ga watan Afirelun da muke ciki.
Ya ce jami’an rundunar yan sandar dake aiki a rundunar ta 9th Mile Division su suka yi uwa suka yi makarbiya wajen chafke matar a kauyen Umulumgbe dake karamar hukumar Udi ta Jihar.
Kakakin Rundunar ya ce mahaifin yaron wanda shine miji ga matar mai suna Justine Egwuagu shi da kan shi ya tsegunta wa rundunar wannan labari inda rundunar ba ta yi wata wata ba wajen chafke ta.
A yanzu haka a cewar shi ana ci gaba da gudanar da bincike don daukar matakin doka kan matar.