By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta, a ranar Talata, ta cafke wanda ake zargi dillalan makamai da harsasai 750 a kan hanyar Nnebisi dake karamar hukumar Oshimili ta kudu na jihar.
Da yake gabatar da wanda ake zargi a Asaba, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Delta, Ali Mohammed Ali, yace an kama wanda ake zargin da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar 5 ga watan Oktoba, 2021.
Shugaban ‘yan sandan ya bayyana cewa wanda ake zargin, Ogorchukwu Mokwe, wanda ya fito daga yankin Ajaji Illah, karamar hukumar Oshimili ta Arewa a jihar Delta, an kama shi a lokacin da ‘yan sintiri na na ofishin Asaba’ dake sintiri yayin da yake dawowa daga Onitsha, Anambra ta jihar.
Rahotannin sun bayyana cewa an kwato harsasai 750 daga hannun wanda ake zargi mai shekaru 28.wanda ake zargin, Ogorchukwu Mokwe yayin da yake zantawa da manema labarai, ya kasa bada takamaiman amsa ga wanda ya sayi harsashin.
Ya kuma bayyana cewa bai samu wani rasit na alburusai da aka saya daga mai sayarwa ba.
A cewarsa“Ni ne na sayi alburusai Ina kai wa Illah ne saboda bikin da muke yi Jami’an ‘yan banga da na’ yan kungiyar asiri suna amfani da harsasai “Mahaifina shine shugaban ‘yan banga a yankin Illah.Na sayi harsashin ne daga babbar kasuwa ta Onitsha. ”