Jami’an tsaron ‘yan sandan Nijeriya a Kaduna sun cafke wadansu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne tare da samunsu da karamar bindiga a hannunsu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Umar Muri ne ya tabbatar da hakan a cikin sanarwar da ya sanyawa hannu, kuma Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Muhammad Jalige ya fitar a ranar Talata a Kaduna.
Umar ya ce an kama wanda ake zargi ne da misalin karfe 8:30 na dare a ranar 2 ga watan Janairun 2021 a gida mai lamba 16 Unguwan Bulus street, Sabon Tasha dake karamar hukumar Chikun a jihar.
Muri ya ce cafke wanda ake zargi, shi wanda aka kama din da tawagarsa an taba zarginsu da addabar yankin da fashi da makami suna yi wa al’ummar yankin kwacen kayayyakinsu.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa wanda ake zargi yana bayar da bayanan da ya kamata wanda zai taimaka musu wajen cafko sauran membobin da ke cikin tawagarsa. Inda ya ce ‘yan sandan na bakin kokarinsu wajen cafko sauran wadanda ake zargi.