By Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Umar Mamman Sanda, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan gawar marigayin, domin bankado al’amuran da suka shafi rasuwar shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Bauchi, Alhaji Musa Hussaini Gwabba.
Sanda a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar, ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu.
Ya ce an kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a kisan kuma an fara gudanar da bincike.
Da take bayyana halin da ya kai ga mutuwar Gwabba, sanarwar ta ce ‘yan sanda sun samu labarin a ranar Asabar cewa Gwabba na cikin damuwa.
“DPO shiyar ofishin yan sanda na (C Division) ya ziyarci wurin da lamarin ya faru a otal din Khairan dake bayan Asibitin Specialist Bauchi, inda ya gana da wanda labarin ya rutsa da su a otal din,tare da garzayawa da shi zuwa asibitin koyarwa na ATBU Bauchi domin yi masa magani, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.
“Bincike na farko ya kai ga kama mutane uku da ake zargi da tare da yi musu tambayoyi”
Ya ce ana dakon sakamakon binciken gawar kuma za a bayyana sakamakon binciken ga jama’a,” in ji sanarwar.