By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta kama wata Anita Yohanna dake dauke da harsashi mai rai a lokacin da take kokarin hawa mota zuwa Yola daga garin Askira dake karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno.
A cewar matashiyar mai shekaru 25 wadda take da shaidar kammala difloma inda tace saurayinta na soja, Lance Kofur Aliyu Isa ne ya bata harsashin domin ta kai wa direban wata motar kasuwanci dake kan hanyar zuwa Yola.
Da take magana a lokacin da rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da wasu mutane 52 da ake zargi, Yohanna tace, “ta yi soyayya da sojan tsawon shekara daya fa wata hudu izuwa yanzu,sannan sunansa Aliyu Isa, Kofur ne tare da sojojin Najeriya dake aiki a Askira.Ya ba ni jakar, ya kuma umarce ni da in kai ta wurin shakatawa a Uba, in sakata a motar da za ta je Yola.
“Na isa filin ajiye motoci na Uba da misalin karfe 5 na yamma. Da na isa wurin direban sai ya tambaye ni abin da ke cikin jakar na ce masa ban sani ba, sai yace mu bude mu tabbatar kafin ya karbi kayan. Bude jakar, keda wuya mun gano harsashi ne mai rai. Mun kirga su, tare da gano harsashi guda 90, a haka aka kama ni aka kawo ni hedikwatar ‘yan sandan jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Sojoji sun kama sojan, yana tsare a yanzu haka a cibiyar sojoji ta Maiduguri.”
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda a jihar Borno, Abdu Umar, ya ce shari’ar Yohanna na daya daga cikin laifuka da dama da ‘yan sanda ke bincike a kansu wadanda suka hada da laifuka hudu da suka hada da fyade da kananan yara da sata da kuma lalata igiyoyin sulke na lantarki.
Kwamishinan ya ce za a gurfanar da dukkan kararrakin zuwa kotu idan an kammala bincike.