- Rundunar ‘yan sandan Zamfara ta bayyana cewa ta ceto yara tara da ‘yan bindiga suka sace.
- A ranar 3 ga watan Yuni, 2023 an samu labari sace yara tara da suka hada da maza da mata.
- Da samun rahoton, rundunar ‘yan sandan hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro sun tattaru zuwa wurin da lamarin ya faru.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta ceto yara tara da ‘yan bindiga suka sace daga al’ummar Gora-Namaye da ke karamar hukumar Maradun a jihar,Punch ta rawaito.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Yazid Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN: NIS Ta Samar Da Fasfo Miliyan 4.5 Cikin Shekaru Hudu – Rahoto
Ya ce, “A ranar 3 ga watan Yuni, 2023, da misalin karfe 20:14 aka samu labari daga Hakimin kauyen Gora-Namaye da ke cikin karamar hukumar Maradun cewa an kama yara tara da suka hada da maza da mata da iyayensu suka tura su debo itace a daji. kuma ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su.
“Da samun rahoton, rundunar ‘yan sandan hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro sun tattaru zuwa wurin da lamarin ya faru inda suka fara aikin bincike da suka kai ga ceto yaran.”
Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa tuni rundunar ‘yan sandan ta sada wadanda abin ya shafa ga iyalansu ba tare da wani sharadi ba.
“Har yanzu ana ci gaba da kokarin zakulo ‘yan fashin domin gurfanar da su gaban kotu,” in ji Abubakar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ce a ranar Asabar din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wasu kauyukan karamar hukumar Maradun inda suka kashe wasu da ba su ji ba ba su gani ba.
A wani labarin kuma, Cire Tallafi: NLC Ta Yi Watsi da Taron FG, Ma’aikatan Wutar Lantarki Zasu Shiga Yajin Aiki
Kungiyar kwadago NLC ta yi fatali da taron da gwamnatin tarayya ta kira domin tattauna batun cire tallafin Fetur.
Ma’aikatan wutar lantarkin sun sha alwashin shiga yajin aikin tare da jefa al’ummar kasar cikin halin kaka-nika-yi.
Kungiyar ta dage cewa ba za ta yi wata tattaunawa da wakilan gwamnati ba, sai an kafa tawaga ta gaskiya.