Zamfara ta ware biliyan 1.95 ga fadar sarakunan gargajiya
Gwamnatin Zamfara ta ware Naira Biliyan 1.95 a cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin sake gina fadar sarakunan jihar 18.
Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautu na jihar Alhaji Ahmad Yandi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Gusau.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kirsimeti: Ku yi addu’a ga gwamnatin Tinubu ta yi nasara – Gwamnan Bauchi ga Kiristoci
Yandi wanda ya bayyana a gaban zama na musamman na kwamitin kudi da kasafin kudi na majalisar ya ce aikin zai kara daukaka martabar sarakunan gargajiya.
A halin yanzu, Gwamna Dauda Lawal a ranar Alhamis ya gabatar da kasafin kudin jihar na Naira biliyan 423.5 ga majalisar domin amincewa.
Yandi wanda ya bayyana a gaban kwamitin don kare kasafin kudin ma’aikatarsa, ya ce yana daga cikin manufofin gwamnati na inganta martabar cibiyar gargajiya a jihar.
Ya kara da cewa “Sauran ayyukan da za a aiwatar a cikin kasafin kudin sun hada da fadada harabar ma’aikatar, da ofishin hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi da sauransu”.
A nasa bangaren, babban sakataren ma’aikatar ayyuka da samar da ababen more rayuwa, Alhaji Shehu Baraya, ya ce an ware sama da Naira biliyan 140 domin gudanar da ayyukan tituna da sauran ababen more rayuwa a jihar.
“Ayyukan sun hada da sake gina manyan tituna a cikin birnin Gusau a karkashin shirin gwamnatin jihar na sabunta birane.
“Gina magudanun ruwa da sauran ayyukan more rayuwa a fadin kananan hukumomi 14 na jihar nan.
“Kudaden da aka ware don ayyukan da ma’aikatar za ta aiwatar na wakiltar kashi 34 cikin 100 na jimillar kasafin 2024 na jihar,” Baraya
A wani labarin kuma:Harin Bam a Kaduna: Yadda Kiristocin Tudun Biri da Musulmi suka yi bikin Kirsimeti a Coci
Al’ummar Musulmi da Kiristan Tudun Biri da ke karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, a ranar Litinin din da ta gabata sun bi sahun duniya domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti tare da gudanar da addu’o’in godiya, kamar yadda kafar yada labarai ta Channels TV ta ruwaito.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Talata 5 ga watan Disamba ne mutanen kauyen ke gudanar da bukukuwan bukukuwan musulmi, wani jirgin yaki mara matuki da sojojin Najeriya ke amfani da shi ya jefa musu bam.