By Abbas Yakubu Yaura
Hukumomi a Burkina Faso sun harba barkonon tsohuwa kan masu gudanar da zanga-zanga a wani gangamin nuna adawa da gwamnati a Ouagadougou babban birnin kasar.
Rikicin ya faru ne a wannan Asabar a yayin da daruruwan masu zanga-zangar suka yi dafifi a Place de la Nation, daya daga cikin manyan filayen birnin.
Jama’ar wadanda suka nuna fushinsu a kan gazawar shugaba Kabore wajen tunkarar tashe-tashen hankula a kasar.
Muzaharar dai ta faru ne sakamakon dakatar da hanyoyin sadarwar wayar salula da aka tsawaita tsawon sa’o’i 96 a ranar Larabar data gabata.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaida da kuma kungiyar da ke da’awar kafa daular Islama sun fara kai ruwa rana a kasar tun shekara ta 2015 inda suka kashe mutane kusan 2000 tare da raba miliyan 1.4 daga gidajensu.