‘Yan sanda a birnin Makkah sun mika wani dan kasar Saudiyya gaban kotu bayan da ake zarginsa da hannu wajen taimaka wa wani Ba’amurke dan jarida wanda ba musulmi ba ya shigacikin birnin Makkah, kamar yadda kakakin ‘yan sandan yankin Makkah ya bayyana.
A cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya fitar a ranar Juma’a, kakakin ya yi cikakken bayani kan lamarin da dan kasar ya yi jigilar dan jaridar zuwa Makkah ta hanyar sadaukar da kai don musulmai.
Ya ce hakan wani karan-tsaye ne na keta dokokin da suka haramta wa wadanda ba musulmi ba shiga cikin harami. An kama dan kasar kuma an dauki matakin shari’a a kansa.
Kakakin ya kara da cewa, akwai bukatar duk masu ziyara a Masarautar su mutunta tare da bin ka’idojin da aka shimfida musamman dangane da Masallatan Harami da wuraren ibada.
“Duk wani cin zarafi na wannan nau’in ana daukarsa a matsayin laifin da ba za a amince da shi ba, kuma za a yi amfani da hukuncin da ya dace ga masu aikata laifuka bisa ga ka’idojin da suka dace,” in ji shi.
Kakakin ya ce an kuma mika shari’ar dan jaridar nan Ba’amurke da ke da hannu a cikin wannan aika-aika ga masu gabatar da kara domin daukar matakin da ya dace a kansa.
Saudi Gazette.
A wani labarin daban
Akalla mutane 30 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Zaria zuwa Kano a jihar Kaduna.
Hatsarin titin wanda ya hada da motocin Toyota bas guda 18 da mota kirar Volkswagen Golf, ya afku ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Alhamis a unguwar Hawan Mai Mashi dake karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna.
Hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da aka yi, wanda ya kai ga haduwae motocin guda uku, bayan da wuta ta tashi.
Yawancin fasinjojin da suka makale a cikin motocin sun kone kurmus, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsu.
Shaidu sun ce wadanda abin ya shafa ba su da hanyar tsira daga motocin.
A cewar mataimakin kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta tarayya dake shiyyar Zariya Abdulrahman Husaini, hatsarin ya faru ne sakamakon hatsaniya da daya daga cikin motocin.
Hussaini ya bayyana cewa an garzaya da wasu fasinjojin da suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Shika domin samun kulawar gaggawa, yayin da aka kwashe gawarwakin wadanda suka mutu aka ajiye a dakin ajiyar gawa na Asibitin.