Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin barayin babura ne a Osogbo, babban birnin jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Wale Olokode ne, ya gabatar da wadanda ake zargin Jelili Jimoh da Olowokere Mojeed a hedikwatar ‘yan sanda da ke Osogbo, babban birnin jihar.
An kama wadanda ake zargin da satar baburan kiran Bajaj a wurare daban-daban a Osogbo.
CP ya ce, ‘yan sandan da ke sintiri sun kama Jelili a unguwar Aregbe bayan da wasu fusatattun mutane suka yi masa kofar Rago, saboda ya kwace babur.
Ya ce an kama Olowokere ne a unguwar Dada Estate, Osogbo inda ya kwace babur din Bajaj mai lamba OSUN AAW 54 DE.
Da yake zantawa da Jaridar Daily Trust, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun saci babur. Sun ce wannan ne karon farko da suka yi kwacen babur.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike.