Rundunar ‘yan sanda a jihar Ekiti ta tabbatar da kama matar wani Fasto da ta gayyaci wani likita don yin lalata wanda a karshe ya mutu a yayin aikata laifin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin mutuwar mutumin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bikin Aure Ya Ruguje Yayin Da Dangin Amarya Da Ango Suka Fafata Kan Dunkulen Magi
Kehinde wani mashahurin likita dan asalin garin Ikere-Ekiti, ya mutu ne a lokacin da suke yin lalata da matar wani malamin addini.
Abutu, da aka tuntube shi ya kara da cewa ‘yan sanda sun kama matar faston.
A cikin kalamansa, “Eh, za mu iya tabbatar da mutuwar mutumin a daya daga cikin otal a Ikere-Ekiti ranar Litinin.
Tuni dai aka dauko gawarsa aka ajiye a dakin ajiye gawa.
“Bari in gaya muku da sauri cewa matar da ake magana a kai tana tare da mu yayin da muke fara bincike don gano musabbabin mutuwar mutumin ko akasin haka,” in ji PPRO.
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Ya Yi Alkawarin Tallafawa Wata Kasa Da Man Fetur Duk Da Karancinsa a Najeriya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kasar za ta tallafawa Jamhuriyar Burundi kan matsalar karancin man fetur don nuna hadin kai da ‘yan uwantaka a Afirka.
A cewar Femi Adesina, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Buhari ya bada wannan tabbacin ne a ranar Talata 3 ga watan Janairu a fadar shugaban kasa dake Abuja, yayin da yake karbar bakoncin manzon musamman na shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye wanda ya zo da sako.