By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama wasu mutane biyu, Aworinde Wale da Olayemi Abiodun, bisa zargin kashe wani direban babur, Ojo Adeyeye a Osogbo dake jihar Osun.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Wale Olokode, ya shaida wa manema labarai cewa wadanda ake zargin sun yi wa Adeyeye fashi ne a unguwar Oke-Osun, suka harbe shi har lahira tare da sace babur din sa na Bajaj.
Olokode ya ce, gungun ‘yan fashi da makami su biyu da suka kware wajen yin fashin babura a Osogbo da kewayen ta, sun kwacewa Ojo Adeyeye babur dinsa na Bajaj a unguwar Oke Osun a Osogbo tare da harbe shi har lahira.”
A lokacin da aka kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda, wata tawagar jami’an tsaron CP’s ta (PRU) ta bi diddigin babur din da aka kwace zuwa Saki ta Jihar Oyo inda suka kwato shi daga hannun mai karba na biyu, Ajibade Faruq, wanda aka kama shi tare da babur din da aka yi fashin.
Faruq ya ce ya sayi babur din ne daga hannun mai karbar na farko mai suna Akeem a kan kudi naira 140,000 a Ibadan.
Babban wadanda ake zargin, Aworinde ya amsa laifinsa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wadanda ake zargin sun sayar wa Akeem babur a kan kudi naira 80,000 kacal sannan Akeem ya sayar wa Faruk.
Olokode ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.