Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta cafke wasu mutane biyu, Chinedu Dioha da Joseph Emmanuel, bisa zargin satar mota da ta kai naira miliyan 15.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Wale Olokode ne ya shaida wa Daily Trust cewa wadanda ake zargin sun sace motar ne a Legas suka kawo Osun domin sayarwa.
An gano motar Mercedes Benz ML 350 mai lamba LAGOS FST 707 GN daga hannun wadanda ake zargin.
Shugaban ‘yan sandan ya ce wadanda ake zargin suna kokarin sayar da motar ne a lokacin da aka kama su a unguwar Molak da ke Ikire.
CP ya ce: “A cikin wani kira da aka samu daga jihar Legas cewa an sace wata mota kirar Mercedes Benz a wani kamfani da ke jihar Legas, sai rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta yi gaggawar tsara dakarunta, inda a lokacin da aka tsaya ana bincike, an kama wadanda ake zargin tare da motar da suka sace. a unguwar Molak dake Ikire yayin neman mai siye. Wadanda ake zargin sun amsa cewa sun sace motar ne daga kamfanin da suke aiki a matsayin ma’aikata.”
Dioha da Emmanuel a zantawar su da majiyar Jaridar Dimokuradiyya sun bayyana cewa sun sace motar ne daga hannun mai aikinsu da ke Legas, inda suka kawo Osun domin sayar da ita.
CP Olokode ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike.