By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wata mata mai suna Bola Agbedimu, mai shekaru 30 a duniya, a ranar masoya, bisa zargin ta da kashe kudaden jabu na naira.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Oyeyemi ya ce an kama wanda ake zargin da kudi naira 1,000 a kasuwar Kila, dake karamar hukumar Odeda ta jihar.
Ya kara da cewa an kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da shugaban kungiyar sayar da amfanin gona na Egbalawa ya mika a hedikwatar ‘yan sanda ta Odeda.
Ya ce, “An shaida wa ’yan sanda cewa an kama wanda ake zargin tana kashe kudi naira 1,000 na bogi a kasuwa. Bayan rahoton, DPO, reshen Odeda, CSP Femi Olabode, ya yi cikakken bayani ga jami’an bincikensa inda ya turasu zuwa wurin da aka kama wanda ake zargin ba tare da bata lokaci ba.
“A binciken da aka yi mata, an gano wasu kudade na bogi na N24,000. A yayin da ake yi mata tambayoyi, wanda ake zargin ta amsa cewa ta saba yin dilan na jabun kudin naira. Ta kara da ikirari cewa tsarin aikinta na hada jabun takardun kudi da na gaske tare da yin amfani da su wajen siyan kaya.
Binciken farko ya nuna cewa an kama ta a lokuta da dama a kasuwanni daban-daban a Abeokuta.”
Sai dai PPRO ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin ga sashen binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.