Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama wasu mutum hudu da ake zargi da laifin hada baki da suka hada da maza biyu da mata biyu da suka kware wajen lalata da kuma karbar kudade daga hannun wadanda abin ya shafa.
DSP Toochukwu Ikenga, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Awka ranar Alhamis din nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ikenga ya ce ’yan kungiyar sun kware wajen daukar hotunan tsiraicin wadanda abin ya shafa tare da yin barazanar sanya su a yanar gizo matukar ba su biya kudi ba.
An Tsare Wani Jirgin Ruwa Da Ake Zargin Na Ɓarayin Danyen Mai Ne
Kakakin ya bayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka; Okechukwu Ogoejiofor, mai shekaru 36, Nonso Nwizu, mai shekara 34, Esther Nwafor lfeanyichukwu, mai shekaru 21 da Obianuju Nduba, mai shekara 20.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a kauyen Ajakpani da ke Umunya a karamar hukumar Oyi bisa laifin hada baki da bata suna da kuma yin sata.
Kakakin ya ce wadanda ake zargin sun yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani wajen jawo mazan su shiga soyayya da abota ta karya sannan kuma suka kai su daki da nufin shigar da su wasan kwaikwayo.