- ‘Yan sanda sun kama wani yaro bayan ya yi fitsari a bayan motar mahaifiyarsa a Mississippi da ke Amurka
- Yaron, Quantavious, yana tare da mahaifiyarsa lokacin da ta je ofishin lauya a Senatobia, Mississippi, kuma an danna shi.
- Bayan Quantavious ya sassauta kansa, ‘yan sanda sun kama shi, daga bisani kuma suka tsare shi, matakin da ya fusata mahaifiyarsa.
‘Yan sanda a Mississippi sun kama wani yaro dan shekara 10 da ya yi fitsari a bayan motar mahaifiyarsa.
Yaron mai suna Quantavious yana tare da mahaifiyarsa a ofishin wani lauya a Senatobia, Mississippi, lokacin da ya ji bukatar yin fitsari.
Quantavious ya yi fitsarin kusa da motar mahaifiyarsa, amma hakan bai yiwa ‘yan sanda dadi ba.
Wani dan sanda ya ganshi yana fitsari ya kama shi. Aka kira mahaifiyarsa, dan sandan ya kyale shi amma ya yi masa gargadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya za ta batar da Naira biliyan 8.63 domin biyan albashi, alawus da duk sauran haƙƙokin ministocin
Mahaifiyar Mississippi ta fusata yayin da ‘yan sanda suka kama danta
Amma wani gungun ‘yan sanda ya zo inda aka tsare Quantavious a gidan yari.
An kai shi ofishin ‘yan sanda na Senatobia kuma an tuhume shi da abin da ‘yan sanda suka kira “yaro mai bukatan hidima.”
Mahaifiyarsa, Latonya Eason , ta mayar da martani:
“A’a, fitsarin da ya yi a wurin ajiye motoci bai yi daidai ba tabbas, amma a lokaci guda na yi amfani da hakan na yiwa yaran maganar kada ya ƙara amma kuma wani jami’in ya kama shi ya kai shi gidan yari. Kamar hakan bai dace ba. Ba ni da magana a yanzu. Me yasa za a kama yaro dan shekara 10?”
Yaron da ‘yan sanda suka kama a Mississippi ya ce ya ji tsoro
Quantavious ya ce yana jin tsoro lokacin da ‘yan sanda suka zo masa:
A Kalamansa:
“Na fara shiga damuwa sosai. Sun kai ni can suka fito da ni daga motar. Ban san me ke faruwa ba. Na tsorata na fara girgiza ina tunanin zan kai gidan yari.”
Daga baya ‘yan sandan sun sako yaron. A cikin wata sanarwa da shugaban ‘yan sandan Senatobia Richard Chandler ya fitar, ya ce kuskure ne a yanke hukunci a kai yaron ofishin.