Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Juma’a ta sanar da kama wasu mutane 62 da ake zargi da laifin fashi da makami da ‘yan daba da safarar miyagun kwayoyi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Abdillahi Kiyawa, ya fitar a Kano.
KARANTA WANNAN: Rufe Kan Iyaka: Najeriya Ba Yaki Zata Yi Da Jamhuriyar Nijar Ba – NCS
Kiyawa ya ce, rundunar ‘yan sandan ta kama wadanda ake zargin ne a yayin gudanar da ayyukan share fage a fadin jihar, Daily Post ta rawaito.
Ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin dauke da muggan makamai da miyagun kwayoyi da kuma wadanda ake zargin sun sace kadarorin jama’a.
Ya ce an gudanar da aikin ne bisa umarnin IGP Kayode Egbetokun ga duk wani tsari na zurfafa aikin ‘yan sandan al’umma don kawar da duk wani nau’in aikata laifuka.
“A bisa wannan ci gaba ne ‘yan sanda suka fara aikin share fage wanda ya share fagen cafke wasu masu laifi a kan Dutsen Dala dake cikin birnin Kano.
“Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da muggan makamai guda 46,kwalabe 253 da ake zargin kodin ne na ruwa,sannan da allurar guda 85 da ake zargin ta sa maye ce, da kuma wasu guda 200 da ake zargin na tsotsa da kuma na mutuwa.
“Sauran sun hada da wasu kunshi guda biyar da ake zargin hodar iblis ce, busasshen ganye kunshi biyar da ake zargin na tabar wiwi ne, da kuma tarin wasu kwayoyi guda 1,802 da ake zargin haramtattu ne, babur mai kafa uku guda daya, da babura biyu,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Kotu Ta Dakatar Da Wani Gwamna Daga Yunkurin Tsige Mataimakinsa
Yanayin siyasa a jihar Edo na daukar wani salo da ba a saba gani ba kamar yadda mataimakin gwamnan jihar, Rt. Hon Philip Shaibu ya garzaya babbar kotun tarayya dake Abuja domin dakatar da shirin tsige shi tare da dakatar da jami’an tsaro da jami’an gwamnan daga tursasa shi.
A cikin takardar karar da aka gani a Benin ranar Juma’a kuma mai lamba FHC/ABJ/CS/1027/2023 tsakanin Rt. Hon. Philip Shaibu wanda shine mai shigar da kara/kuma mai nema da kuma babban sufeton ‘yan sanda, hukumar tsaro ta jihar, gwamnan jihar Edo, kakakin majalisar dokokin jihar Edo da kuma babban alkalin jihar Edo wadanda ake kara a matsayin masu amsa,