Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun mamaye sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a Abuja.
Wannan dai na zuwa ne gabanin kaddamar da shugabannin jam’iyyar na jihohi a yau alhamis.
Wakilin Jaridar Daily trust ya ruwaito daga majiya mai tushe cewa shugabannin jam’iyyar na kasa sun tura ‘yan sanda domin dakile sabawa doka da oda.
Sassan jam’iyyar APC da dama sun shiga cikin rikici biyo bayan sakamakon zaben da aka gudanar a jahohin dake fadin kasar nan a bara.
Daga baya an ba ‘yan jarida izinin shiga cikin ginin sakatariyar amma babu daya daga cikinsu da aka bari ya fita daga ginin.
Babu motsin ababen hawa yayin da ‘yan sanda suka yi amfani da motocin sintiri wajen tare bangarorin biyu na shiga sakatariyar.
Hazuwa da misalin karfe 2:00 na rana ba a fara kaddamar da kwamitin zartaswa na jahohin ba, yayin da shugabannin jam’iyyar ke ci gaba da ganawa da kwamitin riko a bayan fage.