Daga: Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Cross River ta ce ta ceto Miss Josephine Etim Edet, dalibar jami’ar Arthur Jarvis da aka sace a daren ranar Talatar da ta gabata a harabar jami’ar.
A cewar rahoton da ‘yan sanda suka bayar ga ‘yan jarida, rundunar Operation Sting karkashin jagorancin Sufuritandan ‘yan sanda da ake kira Hart ta ceto Josephine daga hannun masu garkuwa da mutane.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/hatsari-ya-hallaka-mutane-30-yayi-sanadin-%c6%99onewar-motoci-a-kaduna/
“Sun kai farmaki maboyar ‘yan ta’addan a Akpabuyo tare da ceto wanda abin ya faru da ita a daren safiyar yau da karfe 01:12.
“Biyu daga cikin masu garkuwa da mutanen sun mutu. An kama daya da rai da munanan raunuka. An garzaya da wanda abin ya shafa da wanda aka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na UNICAL domin yi musu magani,” in ji rahoton halin da ake ciki.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da ceto dalibar.
Ta ce, “Mutanenmu sun kubutar da wanda iftila’in ya afkawa,” ta kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan, ya bayar da umarnin a farauto ‘yan ta’addan tare da nuna godiya ga Allah da aka ceto wanda abin ya shafa da rai.
A Wani Labarin Kuma Kimanin Mutane 30 suka mutu a wani Hatsarin mota da ya faru akan hanyar Zaria zuwa Kano a ranar Alhamis.
Lamarin ya faru da misalin Karfe 5:30 na yamma kusa da Hawan Mai Mashi a karamar Hukumar Makarfi dake Jahar Kaduna.
Mataimakin Shugaban Hukumar Mai kula da kiyaye Hadurra ta kasa reshen Shiyyar Zaria, Abdurrahaman Yakasai, ya tabbatarwa Daily Trust da faruwar lamarin .
Ya bayyana cewa, Haɗari ya rutsa da motoci biyu masu cin fasijojin 18 na motar Toyota tare da ƙirar Volkswagen Gulf, ya Kara da cewa Hatsarin ya faru sanadiyyar mugun gudu da mummunan daukar hannu da motocin ke yi.
Ya bayyana cewa, ” waɗanda suka ji raunuka an hanzar ta Kai su Asibitin Koyar wa na Shika dake Zaria, yayin da aka Kai matattun wurin Adana gawa ta asibitin.”
Kwamandan yace FRSC har yanzu bata gano cewa Lambobin motocin domin tuni an ƙone su.
Amma yace ana ƙoƙari domin gano bayanan waɗanda lamarin ya rutsa dasu.