Rundunar ‘yan sanda a jihar Borno ta dakile wani harin bam da mayakan Boko Haram da kungiyar IS suka binne a sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori da ke jihar Borno.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdu Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani taron manema labarai a Maiduguri ranar Alhamis.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori, a karamar hukumar Konduga yana da tazarar kilomita kadan daga Maiduguri, akan hanyar Maiduguri zuwa Bama.
NAN ta kuma ruwaito cewa lamarin ya faro ne da misalin karfe 6:00 na safe, inda aka ga wani abu da aka boye a cikin buhu wanda ake zaton na’urar fashewa ne, lamarin da ya sanya mazauna sansanin suka bar matsugunin su suka gudu.
Umar ya ce nan take aka aike da jami’an hukumar zuwa wurin domin kwance abun fashewar Wato IED.
“An gano wani abu da ba a san ko wanene ba da ake zargin abun fashewa ne samfarin IED, da aka dasa a cikin bokitin roba tare da wani murfi kusa da shingen sansanin da ake zargin ‘yan tada kayar baya.ne suka dasa shi.
“Rundunar kwance abubuwan fashewa ta EOD ta samu nasarar dakile harin Bam din ba tare da haddasa asarar rayuka ba,” in ji shi
Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa, an tabbatar da tsaro a yankin gaba daya, inda ya bukaci jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullun.