Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) su hudu ranar Litinin.
Mayakan na aiki ne a karkashin kungiyar IPOB masu dauke da makamai, domin Neman kafa kasar Biafra.
An yi artabu da bindiga a Amaifeke da Ihioma na karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.
Dakarun rundunar ta 34 Brigade Obinze sun mayar da martani bayan da maharan suka yi ta harbe-harbe, lamarin da ke barazana ga rayukan ‘al’umar jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce ’yan kungiyar sun bude wuta ne a lokacin da suka ga tawagar sintirin jami’an Yan sandan.
Nwachukwu ya Kuma kara da cewa sojojin sun yi artabu da su, inda suka kashe hudu yayin da wasu suka tsere daga wurin da suka kawo harin.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da bindiga guda daya, harsashi masu kisa guda 10 da kuma wata mota kirar Toyota Hilux.
An kwace motar da bindiga tun da farko. An kuma samu wayoyin hannu da laya a hannun maharan na IPOB.
Sojojin sun umurci mazauna garin da su ba da sahihin bayanai kan motsin “masu aikata laifuka zuwa hukumomin tsaro a duk lokacin da aka gansu”.
A wani labarin Kuma na daban.
Yan sanda sun kwance bam a sansanin ‘yan gudun hijira dake Borno
Rundunar ‘yan sanda a jihar Borno ta dakile wani harin bam da mayakan Boko Haram da kungiyar IS suka binne a sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori da ke jihar Borno.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdu Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani taron manema labarai a Maiduguri ranar Alhamis.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori, a karamar hukumar Konduga yana da tazarar kilomita kadan daga Maiduguri, akan hanyar Maiduguri zuwa Bama.
NAN ta kuma ruwaito cewa lamarin ya faro ne da misalin karfe 6:00 na safe, inda aka ga wani abu da aka boye a cikin buhu wanda ake zaton na’urar fashewa ne, lamarin da ya sanya mazauna sansanin suka bar matsugunin su suka gudu.
Umar ya ce nan take aka aike da jami’an hukumar zuwa wurin domin kwance abun fashewar Wato IED.
“An gano wani abu da ba a san ko wanene ba da ake zargin abun fashewa ne samfarin IED, da aka dasa a cikin bokitin roba tare da wani murfi kusa da shingen sansanin da ake zargin ‘yan tada kayar baya.ne suka dasa shi.
“Rundunar kwance abubuwan fashewa ta EOD ta samu nasarar dakile harin Bam din ba tare da haddasa asarar rayuka ba,” in ji shi
Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa, an tabbatar da tsaro a yankin gaba daya, inda ya bukaci jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullun.
Comments 1