By Ishaq Dabai
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sanda SP Muhammad Shehu, ya bayyana a cikin wata sanarwa daya fitar a Gusau, ranar Alhamis cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta mika jimillar mutane 187 da aka ceto wadanda suka hada da maza, mata manya da kananan yara ga gwamnatin jihar.
“Bayan aiwatar da sabbin matakan tsaro da gwamnatin jihar Zamfara tayi, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro suna kai hare hare kan wuraren da aka gano ‘yan bindiga a sassa daban daban na jihar, da nufin kawar da jihar daga dukkan ‘yan ta’adda da sauran abubuwan laifi.
“A yau 7 ga Oktoba, 2021, jami’an ‘yan sanda na hadin gwiwa a dajin Tsibiri dake karamar hukumar Maradun, sun yi nasarar ceto mutane 187 da aka sace a Rini, Gora, Sabon Birni da Shinkafi a Bakura Maradun da Karamar Hukumar Shinkafi bi da bi.
“Wadanda aka sace, sun shafe makwanni da dama a hannun masu garkuwa da mutane, an kubutar dasu ba tare da wani sharadi ba bayan wani gagarumin aikin bincike da ceto da aka dauki tsawon awanni ana yi,” in ji Shehu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Ayuba Elkanah, yayin da yake mika wadanda aka ceto ga Gwamna Bello Matawalle, yace sabbin matakan tsaro a jihar suna haifar da sakamako mai yawa, saboda hakan ya kai ga nasarar kubutar da daruruwan wadanda aka sace.kazalika, an kama ‘yan fashi da dama tare da abokan aikinsu, an gurfanar da wasu a gaban kotu, yayin da wasu ke gudanar da bincike cikin hikima, in ji Shehu.
A halin yanzu, Elkanah ya ba da tabbacin cewa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da yin iya bakin kokarinsu don tabbatar da dawowar dawwamammen zaman lafiya da tsaro a jihar
Da yake mayar da martani, a lokacin da yake karbar wadanda aka ceto, Matawalle ya godewa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro saboda jajircewa da aiki tukuru wajen aiwatar da sabbin matakan tsaro a jihar.
Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe ya wakilta, ya bada tabbacin ci gaba da bada goyon baya ga gwamnatin jihar ga hukumomin tsaro a jihar, don ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.