Daga: Ibrahim Hassan Hausawa
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun cafke daya daga cikin fursunonin, wanda ya tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja, sakamakon harin ta’addanci da aka kai ginin a ranar Talata, 5 ga watan Yuli, 2022.
An kama matashin mai shekaru 28 da haihuwa, mai suna Yakubu Abdul-Mumuni a Sango-Ota, karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar, biyo bayan wani labari da rundunar ‘yan sanda ta samu a hedikwatar Sango Ota da ke cewa an ga mai laifin a kewaye wani wuri dake yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/zaa-yi-ruwa-kamar-da-bakin-kwarya-a-wasu-sassan-kasar-nan-nimet/
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da kamun, ya ce an kama wanda ya gudu ne a ranar Litinin, kwanaki biyu bayan bikin babbar sallah.
“Bayan samun labarin, DPO sashin Sango Ota, SP Saleh Dahiru, yayi gaggawar tattara mutanensa, suka koma yankin da aka kama wanda ake tuhuma,” in ji Oyeyemi.
Ko da yake cikakkun bayanai na yadda dan tseren ya samu hanyar zuwa Kudu maso Yamma kafin daga karshe a cafke shi a Sango Ota, amma Oyeyemi, ya bayyana cewa wanda ya tsere ya shaida wa ‘yan sanda cewa lallai ya tsere daga cibiyar gidan yarin Kuje lokacin da aka kai hari wurin makonni biyu da suka wuce.
Ya kara da cewa wata babbar kotun jihar Kogi ta same shi da laifin hada baki da kuma kisan kai, inda aka tura shi gidan yari na Kuje dake Abuja.
PPRO ya kuma bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, ‘Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a gaggauta mika wanda ya gudu zuwa sashin binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar (SCIID) domin saukaka masa hanyar zuwa gidan gyaran hali da tarbiyya na Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja.
Binciken JARIDAR DIMOKURADIYYA ya nuna cewa wanda ya tsere, Abdul-Mumuni, ba ya cikin fursunoni 69, wanda shi ma ya tsere daga gidan yarin, kuma hukumar da ke kula da gidajen yari (NCoS) ta bayyana cewa tana neman sa a shari’ar ta’addanci.