By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan Afirka ta Kudu a ranar Talata ta bayar da rahoton cewa, ta kama wasu masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba su kimanin 77 daga ranar 14 zuwa 18 ga watan Afrilu a garin Orkney da ke lardin Arewa maso Yamma bisa laifin hakar ma’adinai ba tare da lasisi ba.
Rundunar ‘yan sandan ta ce, wata tawagar ‘yan sanda mai ladabtarwa da kuma tawagar ceton ma’adanai sun kaddamar da farmaki kan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba tare da kame wasu daga karkashin kasa bayan da suka nemi agaji a lokacin da wasunsu suka makale a karkashin kasa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan lardin Arewa maso Yamma, Sabata Mokgwabone, ya ce “aikin ya biyo bayan bukatar da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida suka yi wa jami’an ma’adinan na a taimaka musu su fita daga ramin hakar ma’adinan saboda suna cikin yunwa.
“A yayin aikin da aka gudanar a yankin Shaft no. 5, a Orkney, masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne suka kawo gawarwakin mutane hudu a ranar 15 ga watan Afrilu, 2022.
“A cikin masu hakar ma’adinai 77 da aka kama, wadanda aka duba lafiyarsu, 60 daga cikin su ‘yan kasar Lesotho ne, yayin da 13 daga Mozambique, hudu kuma ‘yan kasar Zimbabwe ne.
A halin da ake ciki, ana ci gaba da gudanar da aikin tantance gawarwakin mutanen hudu.’’
Mokgwabone ya ce wadanda aka kama ba bisa ka’ida ba za su gurfana a gaban kotu a ranar Talata suna fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba da kuma saba dokar shige da fice.
Baki daga kasashen da ke makwabtaka da kasashen ketare da ke fuskantar kalubalen tattalin arziki na ta kwararowa zuwa Afirka ta Kudu domin neman wuraren kiwo. Wasu suna aikata laifuka yayin da wasu ke zuwa mahakar ma’adinan da aka watsar don yin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Xinhua/NAN
Comments 1