‘Yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun yi zanga-zangar lumana da nufin tilasta wa gwamnatin Nijeriya sako Shaikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa.
Sun gudanar da zanga-zangar ne domin neman bukatar gwamnatin Nijeriya hanzarta sakin jagoransu Sheikh Ibraheem Yakub El-Zakzaky da mai dakinsa, wadanda ke daure a gidan kurkukun jihar Kaduna yau tsawon watanni.
Da yake magana da manema labarai kan dalilansu na fitowa zanga-zanagar, daya daga cikin mabiyan Malamin, Sheikh Aliyu Umar Turmizy ya shaidawa wakilinmu cewa; dalilansu na fitowa yin tattaklin a ranar Juma’a shi ne; “muna bukatar ganin gwamnatin jihar Kaduna ta sako jagoransu ne biyo bayan wata kotu a Nijeriya da ta umurci yin haka tun daga farko.” Inji shi.
Masu zanga-zangar dai sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakan kare kashe-kashen al’umma a yankin Arewacin Nijeriya.