By Ishaq Dabai
Matafiya dake kan layin dogo daga Kaduna zuwa Abuja a daren Laraba sun godewa Allah da suka tsira yayin da bam din da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa a cikin jirgin su, wanda hakan ya tilasta musu kaucewa hanya.
Faruwar lamarin keda wuya Nan da nan ruwan harsasai ya biyo baya wanda ya farfasa gilashin motar direba, yayin da masu rakiyar ‘yan sanda, a bayyane suka fi yawa, sun ba da juriya akan lamarin.
Kamfanin jiragen kasa na Najeriya, NRC, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya, inda yace jirgin ya bar tashar Rigasa, Kaduna zuwa Abuja da yamma lokacin da bala’i ya afku.
Manajan Darakta na NRC, Injiniya Fidet Okhiria, ya yi bayanin cewa abubuwan fashewar sun lalata hanyoyin dogo a wani wuri tsakanin Dutse da Rijana, a sashin Kaduna.
Sannan ya kara da cewa: “Ee, akwai fashewar abubuwa a kan hanyar jirgin kasa a wani wuri kusa da Rijana da Dutse a daren jiya, kuma wannan ya lalata hanyoyin.
“A halin yanzu ana ci gaba da kokarin ganin an dawo da ayyukan jirgin kasa dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.” Da yake musanta rahotannin dake cewa an yi harbe-harbe ne kan direban jirgin, Okhiria yace: “Babu wani abu makamancin haka, kawai abin fashewa daya fashe a kan hanya.
“Direban ya sha wahalar tafiya zuwa tashar Rigasa ta Kaduna. Da sanyin safiyar nan (jiya), ina cikin jirgin lokacin da jirgin namu ya ci karo da wani abin fashewa daya lalace.
Comments 1