By Ishaq Dabai
Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da Naira miliyan 97 don tallafawa kungiyoyin kwallon kafa 47 dake buga gasar League, Kwamishinan Yada Labarai, Muhammed Garba,shine ya bayyana hakan .
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Kano, Garba yace asusun zai taimaka wa kungiyoyin masu son shiga gasar ta 2021/2022 da aka shirya farawa a watan Nuwamba.
A halin da ake ciki, majalisar ta kuma amince da Naira miliyan 55 don siyan STB don samun nasarar canzawa daga tsohon yayi zuwa talabijin na zamani a jihar.
Garba yace za a canza daga ranar 30 ga watan Oktoba, lokacin da masu amfani da talabijin za su bukaci STB na zamani don samun alamar tashar ta TV.
Kwamishinan yace majalisar ta umarci Ma’aikatar Karamar Hukuma da Harkokin Masarautu dasu shawo kan lamarin.
Ya kara da cewa ma’aikatar zata samar da STB ga dukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, cibiyoyin duba al’umma, hukumomin ilimi na karamar hukuma, makarantun firamare da na asali da kananan hukumomi 44 na jihar.
Za a kuma samar da wani bangare 7,000 na STB ga Ma’aikatu da Hukumomi 114 da 1,460 zuwa Manyan Makarantun Sakandare a jihar a kan kudi Nsira 12, 500 kowace sashi, ”in ji shi.