Rundunar sojin Najeriya ta ce rahotannin da aka samu game da hare-haren da ‘yan awaren Kamaru (Ambazonian) sun kai wa wasu kauyuka hari, karya ne tsagwaranta
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya.-Janar. Onyema Nwachukwu ne ya fitar da sanarwa a ranar Litinin.
Nwachukwu ya ce sojojin Najeriya da ke garin Danare sun samu bayanai tare da tattarawa al’ummar Bashu, wadanda ake zargin an kai musu hari.
Kakakin ya kara da cewa da isar su sun gano cewa babu wani kutse ko hari da aka yi a Bashu.
“A maimakon haka, ‘yan awaren sun kai hari Obonyi 2 da Njasha, wadanda dukkansu al’ummomi ne a Jamhuriyar Kamaru,” in ji shi.
Mutane hudu da lamarin ya rutsa da su, wadanda Yan Najeriya ne, sojoji da jami’an Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) sun ceto su.
Nwachukwu ya bada tabbacin baiwa sojoji kariya sannan ya shawarci jama’a da su kwantar da hankalinsu.
A wani labarin Kuma na daban
Jami’an tsaro sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana a wani shingen binciken ababan hawa da ake kira MILTAKWAS a karamar hukumar Jibia a jihar Katsina sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a yau Litinin.
Sakamakon harin Ababan hawa uku ne suka Ƙone, kuma Majiyarmu ta bayyana cewa, biyu daga cikin motocin na hukumar kwastam ne da kuma hukumar shige da fice ta ƙasa.
Ƴan bindigar sun isa shingen binciken ne a kan babura sama da hamsin cikin tsakar dare, kuma jim kadan bayan sojojin da ke sintiri suka tashi zuwa garin Jibia biyo bayan bayanan sirri da suka samu na cewa ‘yan bindigar sun nufi garin ta wata kusurwa.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kona motocin tare da lalata wasu kayayyakin da aka gano a shingen binciken kafin su koma dajin.
Kakakin Hukumar Kwastam ta Najeriya a Katsina Isah Danbaba ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “Eh, an kai hari. Daga cikin rahoton da muka samu, maharan sun kona motocin aiki guda biyu da wata mota ta wani jami’in.
“Daya daga cikin motocin na Hukumar Kwastam ne yayin da daya kuma na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ce.
Yayin da muke magana, muna kan hanyarmu ta zuwa wuri,” inji Danbaba.