Rahotanni daga jihar Kano na nuna cewa, Tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP mai adawa a wannan rana ta Talata.
Ya bayyana hakanne ta cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazabarsa ta Kwankwaso da ke karamar hukumar Madobi a jihar Kano.
A wani labarin Kuma na daban
Harin Jirgin Ƙasa: Shugaban Soji ya ziyarci wurin, ya umarci Sojoji su kamo Maharan da suka aikata lamarin
Shugaban Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya ya umarci Dakarun Soji da su cigaba da nemo waɗanda aka kama a hari Jirgin Kasa na Kaduna, tare da kamo Maharan.
Shugaban Sojin ya bada umarnin a lokacin da ya ziyarci wurin da aka hari Jirgin Kasa a Kaduna a ranar Talata.
Wannan na Ƙunshe ne a cikin wata Sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojin Birgediya-Janar Onyeama Nwachukwu mai take “Shugaban Sojin Ƙasa yakai ziyarar duba wurin da aka kai harin Jirgin Ƙasa na Kaduna-Abuja.
Sanarwar tace “Shugaban Sojin Ƙasa wanda ya samu rakiyar wasu manyan jami’an Soji na Hedikwatar da Janar dake kula da yankin, inda suka duba yanayin tsaron wurin, da kuma harin gami da wajen Jirgin Ƙasa domin duba yanayin Lalacewar wurin.
“Ya baiwa Dakarun Sojin umarni da sauran Hukumomin tsaro da su cigaba da bincike tare da ceto waɗanda suka sace.
“Shugaban Sojin ya kuma baiwa ƴan Najeriya tabbacin cewa, Dakarun Soji a shirye suke wajen yaƙi da ƴan bindiga da dukkanin ta’addanci a Ƙasa.
“Ya yi kira ga Al’umma dasu cigaba da baiwa Sojoji bayanan sirri domin inganta ayyukan su a faɗin Ƙasar nan.