YANZU-YANZU: Ƴan Bindiga sun shiga gidaje da dama a Kaduna, sun sace Mutane
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mazauna unguwar Keke B kimanin mutane 36 mazauna garin Millennium a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Lamarin dai, kamar yadda wakilinmu ya gano, ya faru ne a daidai lokacin da jama’a da dama ke shirin yin bacci a ranar Litinin
.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jahar Edo ta Tabbatar da Mutane 8 da suka kamu da Cutar Ƙyandar Biri
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa ƴan fashin da suka yi aikin ba tare da ƙalubalantar su ba, sun rika tafiya gida gida.
A cewar Muhammad Salihu, wani mazaunin garin, “Da yawa daga cikinmu muna waje lokacin da ƴan bindigar suka kai hari da misalin ƙarfe 8:30 na dare.
“Sun zo da adadi mai yawa, suna ta harbe-harbe. Sun kutsa cikin gidajen mutane ɗaya bayan ɗaya tare da yin garkuwa da mutanen.
Mutum daya mai kanikancin babur ya iya tserewa daga hannun masu garkuwa da mutane, amma sun tafi tare da mazauna 36.”
Kawo yanzu dai babu wani bayani a Hukumance daga Hukumomin Tsaro har zuwa lokacin da wannan rahoto ya fito. Wakilinmu ya tattaro cewa a halin yanzu jami’an ‘yan sanda na cikin jama’a domin ganin lamarin ya faru.
Daily Trust ta gano cewa wata ɗaya da ya gabata ne aka yi garkuwa da wasu mazauna unguwar guda bakwai da suka haɗa da wani mutum da matarsa da kuma ƴan aikinsu.