- Shugaban kasa Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa birnin Paris domin halartar taron Paris kan Sabuwar Yarjejeniyar Kuɗi ta Duniya
- Wannan itace ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje a matsayin shugaban kasa
- Shugabannin za su yi la’akari da damammaki na maido da harkokin kudi ga kasashen da ke fuskantar kalubalen kudi na gajeren lokaci
Shugaban kasa Bola Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa birnin Paris domin bin sahun takwarorinsa shugabannin duniya don halartar taron Paris kan Sabuwar Yarjejeniyar Kuɗi ta Duniya, Punch ta rawaito.
Jirgin saman Gulfstream na Tinubu ya tashi ne da misalin karfe 11:30 na safiyar Talata a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe a ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje a matsayin shugaban kasa.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Ɗumi: Tsohon Gwamnan PDP a Arewa Ya Shiga Hannun EFCC
Taron na kwanaki biyu, wanda shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai karbi bakunci, zai gudana ne a Palais Brongniart, daga ranakun 22-23 ga watan Yunin 2023.
Yayin da yake a birnin Paris, shugaban zai “yi, nazari da rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar hada-hadar kudi ta duniya.
Yarjejeniya wacce ke sanya kasashe masu rauni a jerin fifiko don bada tallafi da saka hannun jari,sakamakon mummunan tasirin sauyin yanayi, matsalar makamashi, da kuma bayan tasirin cutar COVID-19.”
Wata sanarwa da mai ba da shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake ya sanya wa hannu, ta karanta a ranar Litinin.
Shugabannin za su yi la’akari da damammaki na maido da harkokin kudi ga kasashen da ke fuskantar kalubalen kudi na gajeren lokaci, musamman ma wadanda suka fi fama da bashi.
Shugabannin kuma za su yi amfani da sabbin hanyoyin samar da kudade ga kasashen da ke fama da sauyin yanayi; samar da ci gaba a cikin kasashe masu karamin karfi.
Kazalika da karfafa zuba jari a cikin kayayyakin more rayuwa don canjin makamashi a cikin kasashe masu tasowa.
A cewar Alake, Shugaban da sauran shugabannin duniya, cibiyoyi daban-daban, masana harkokin kudi da masana tattalin arziki suma za su yi nazari sosai kan farfado da tattalin arzikin kasashe daga tasirin annobar COVID-19.
Sannan da kuma yin nazari kan karuwar talauci, tare da hangen nesa don ba da damar samun kuɗi da saka hannun jari wanda zai ba da damar ci gaba mai ma’ana.
Tinubu, wanda zai dawo a ranar Asabar, zai samu rakiyar mambobin majalisar ba da shawara kan manufofin shugaban kasa da kuma manyan jami’an gwamnati.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: An Zabi Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi
Abubakar Suleiman ya sake zama shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi
An zabi Suleiman a natsayin kakakin majalisar dokokin Bauchi ba tare da wata hamayya ba
Dukkansu an zabe su ne a wajen kaddamar da majalisar ta 10