Akwai jami’an tsaro sosai a babban bankin Najeriya (CBN), reshen Abeokuta.
Yan sanda da sanyin safiyar ranar Litinin, sun tura jami’ansu zuwa reshen bankin Apex da ke Okelewo, Abeokuta domin dakile yiwuwar kai hare-hare daga masu aikata laifuka.
KARANTA WANNNA LABARIN; FBI, Da ‘Yan Sanda Na Farautar Wadanda Suka Yi Ajalin Matar Faston Najeriya
An ruwaito cewa akwai wani rahoton sirri da ke cewa wasu mutane na iya kaiwa bankin hari saboda rashin samun damar mallakar sabbin takardun naira da aka yi wa kwaskwarima.
Wakilin majiyar Dimokuradiyya ya ruwaito cewa an ajiye ‘yan sanda dauke da makamai a wurare masu mahimmanci don hana tabarbarewar doka da oda.
Haka kuma, wasu bankunan kasuwanci a Abeokuta sun hana shiga harabar su saboda fargabar fusatattun kwastomomi su ka iya kai musu hari.
A yawancin bankuna, ana ba abokan ciniki damar yin amfani da na’urar ciran kudi na (ATM) maimakon shiga cikin banki.
An ruwaito cewa, an samu rahotanni makamancin haka a wasu sassan kasar nan a makon da ya gabata.
A halin yanzu, kwastomomi na cikin layi suna jiran cire kudi daga na’urorin ATM.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa har yanzu karancin kudin Naira na ci gaba da ci gaba da ci gaba da tabarbarewa a jihar Ogun, lamarin da ya shafi harkokin kasuwanci da dai sauransu.
A wani labarin kuma, Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Koli, Da Ta Baiwa Lawan Tikitin Takara
Tsohon dan majalisar Dattawa Najeriya, Sanata Shehu Sani, ya mayar da martani kan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Litinin, wadda ta mayar da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar APC, mai wakiltar Yobe ta Arewa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Sani ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter.