An kashe mutane 7 a kauyen Mmaahu da ke karamar hukumar Ohaji Egbema ta jihar Imo a wani tashin tashina da ya hada wasu kungiyoyin asiri guda biyu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, rikicin ya barke ne tsakanin kungiyoyin asiri na De-Gbam da De-Well.
‘Yan sanda sun ce a ranar 08/02/2022 da misalin karfe 10 na dare wasu mutane 20 dauke da makamai karkashin jagorancin Ossy da suka rufe fuskokinsu, suka mamaye yankin, inda suka je gidan wadanda abin ya shafa suka harbe su har lahira.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya bayyana sunayen wadanda harin ya rutsa da su, Charles Mgbarahor, Funky Anane, Charity Nwachukwu, Edeme Okoro, Isaac Ojenya, Ndubuisi Nwabusi, da kuma Junior Ifeyinwoke.
Abattam ya ce jami’in ‘yan sandan shiyya ya samu wannan bayanin nan take ya tattara mutanensa da sauran tawagar ‘yan sintiri zuwa yankin, da isar su Kuma ‘yan bindigar suka bar wurin, bayan sun kashe Mutum 7.
Ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa kisan na da alaka da kungiyar asiri.
Abattam ya ce rundunar ‘yan sandan ta tura karin wasu jami’ai zuwa ga al’umma domin tallafa wa aikin rundunar ‘yan sanda da na jami’an Sakai na Egbema domin dakile ayyukan ta’addanci a yankin.
Comments 1