Mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talatar nan ya yanke wa babban Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan Usman Baba hukuncin daurin watanni uku a gidan yari saboda ya ki bin umarnin kotu.
Mai shari’a Olajuwon wanda ya yanke hukuncin ya ce umarnin ya biyo bayan karar da wani tsohon jami’in ‘yan sanda, Patrick Okoli ya shigar inda ya ce ya yi ritaya daga aikin ‘yan sandan kasar ba bisa ka’ida ba akan tilas. Kamar yadda jaridar Daily Post ta rawaito.
A Wani Labarin Kuma Zan Ci Gaba Da Faɗawa Shugabanni Masu Mulki Gaskiya – Sultan
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ce zai ci gaba da fadin gaskiya a kan masu mulki duk da cewa wasu ‘yan siyasar Najeriya ba su ji dadi.
Ya kuma bukaci shugabanni da su dauki shawararsa a matsayin wanda ya damu da jin dadin jama’a.