By Ishaq Dabai
Gabanin babban taron zabubbuka na kasa na ranar 31 ga watan Oktoba na jam’iyyar PDP, shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga Arewa ta Tsakiya, a daren Talata, sun amince da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Iyorchia Ayu, a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa baki daya.
Ayu ya samu goyon bayan gwamnan jihar Benue, wanda shine mataimakin shugaban kwamitin shiyya na PDP Dakta Samuel Ortom.sannan kafin haka Ortom bayan wasu makwanni ya neman goyan bayan wani tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya juya ga Ayu sakamakon zargin adawa da wasu manyan jiga -jigan jam’iyyar.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a wurin taron, Gwamna Ortom yace “Wannan taron masu ruwa da tsaki ne na Jam’iyyar PDP ta Arewa ta Tsakiya don ci gaba da nemo dan takarar da zai zama shugaban jam’iyyar na kasa baki daya.“Muna neman wanda ke da iyawa, jajircewa, soyayya da son jam’iyyar mu.Mun hadu a nan na awanni da yawa kuma cikin mutane biyar dake fafatawa.
“A matsayinmu na shugabancin jam’iyyarmu daga Arewa ta Tsakiya, mun amince baki daya don daukar nauyin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Iyorchia Ayu, don ya zama Shugaban Jam’iyyarmu ta Kasa.
Kazalika yace“(yau, Laraba), masu ruwa da tsaki na arewa na jam’iyar PDP zasu gana. Don haka za a gabatar da shi ga kungiyar arewa ta jam’iyyar
Taron ya samu halartar tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki; tsohon Ministan Yada Labarai, Farfesa Jerry Gana; tsofaffin gwamnonin jihohin Neja, Kogi da Kwara, Babangida Aliyu, Ibrahim Idris da Abdulfatai Ahmed, da dai sauransu.