A sanyin safiyar Yau Laraba ne Wani abun fashewa ya tarwatse a wata Masallaci a Kabul Babban birnin kasar Afghanistan dake kusa da Ma’aikatar kula da harkokin cikin gida na kasar mai dauke da tarin jama’a.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito Kakkakin Ma’aikatar Abdul Nafi Takor na cewa, Masu ziyara ne ke amfani da Masallacin da kuma akasarin Ma’aikatan Ma’aikatar ta kula da harkokin cikin gida.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yayin Da Ake Fama Da Ambaliyar Ruwa A Wasu Jihohi, NiMet Ya Yi Sabbin Hasashen Yanayi
Sai dai gwamnatin kasar ba ta bayyana abin da ya haddasa fashewar din ba bam a birnin Kabul, inda masu kaifin kishin Islama suka kai hare-hare a ‘yan watannin nan.
Kana Kungiyar agaji ta mai zaman kanta NGO ta Italiya da ke kula da asibiti a Kabul, ta bayyana a shafin Twitter cewa ta karbi majinyata 20 daga cikin wadanda fashewar ta shafa, wadanda biyu daga cikinsu sun mutu yayin da suka isa asibitin.
Filin ma’aikatar cikin gida na cikin wani wuri mai tsaro kusa da filin jirgin saman Kabul.
Kungiyar Taliban da ke mulkin kasar ta ce ta tabbatar da tsaron kasar tun bayan da ta karbi ragamar mulkin kasar a shekarar 2021 bayan shafe shekaru goma ana tada kayar baya. Sai dai ko da yake an kawo karshen fadan da ake gwabzawa, amma an samu tashin bama-bamai a wasu birane a cikin ‘yan watannin nan.
Idan za a iya tunawa ko a ranar 12 ga watan Agustan shekarar nan, Rahotanni sun nuna cewa, mutum 21 sun mutu yayin da wasu 33 suka sami mummunan raunuka bayan tarwatsewar wani Bam a wata masallaci dake Kabul babban birnin kasar ta Afghanistan yayin sallar La’asar.
A WANI LABARI KUMA: Bayan Juyin Mulki, Tawagar ECOWAS Ta Isa Burkina Faso
Yayin da ake cigaba da zaman tar tar a Burkina Faso bayan juyin mulki da akayi a kasar, tawagar Jami’an kungiyar Afrika ta Yamma da ta je duba halin da ke ciki a kasar. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Tawagar a ranar Talata ta gana da Capt Ibrahim Traoré, shugaban sojoji wanda a ranar Juma’a ya hambarar da gwamnatin Laftanar Kanar Paul-Henri Damiba, wanda ya hau karagar mulki a watan Janairun wannan shekarar.