Hukumar kula da hasashen Yanayi ta ƙasa (NiMET) ta yi hasashen cewa za’a samu haskawar rana da gajimare daga yau laraba zuwa Jumu’a a faɗin ƙasar nan. Kamar yadda Daily Trust ta ruwiaito.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwiato ce, Hasashen yanayin hukumar da aka fitar a ranar Talata a babban birnin Tarayya Abuja ya nuna cewa za a samu haskawar rana da gajimare a arewacin Nijeriya tun daga yau Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bayan Juyin Mulki, Tawagar ECOWAS Ta Isa Burkina Faso
Hukumar tace za a samu tsaawa a sassan jihohin Kaduna, Gombe, Bauchi, Taraba da Adamawa, haka kuma ta bayyana cewa za a samu yanayi na hadari da kadawar iska a jihohin Kebbi ,Naija, Kano da babban birnin tarayya Abuja, Borno da kuma jihar Zamfara.
Dimokuradiyya ta nakalto cewa, Hukumar, tace har yanzu yankin a rewacin Najeriya da kudanci ƙasar nan na cikin fargabar samun ambaliyar ruwa.
Hukumar tayi kira ga kamfunan jiragen sama da suyi ƙoƙarin samun sababbin bayanan da hukumar ta fitar yayin gudanar da ayyukan su.
A WANI LABARIN KUMA: Wani Shagon Siyar da Kayan Daki Ya Kama Da Wuta A Kano
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da tashin Wata gobara, a shagon siyar da kayan daki da kujeru, dake kan titin Murtala Muhammad a cikin kwaryar birnin Kano.
Mai magana da yawun Samun Abdullahi Yusif ne ya tabbatar da hakan, a zantawarsa da Dimokuraɗiyya, yana mai cewa sun samu kiran waya da misalin karfe 10:58 na safe, inda ake sanar musu da tashin wutar a shagon na Vava Furniture.