Shugaban kwamitin riko da tsare-tsare na musamman na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana cewa za a gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa a ranar 26 ga watan Fabrairu.
Buni ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja yayin da yake gabatar da jawabi a wurin taron mata na Progressive Women Congress da ake gudanar a Babban Birnin Tarayya.