Akarshe dai gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele, a ranar Talata ya gurfana gaban kwamitin majalisar wakilai, inda yake binciken yadda aka canza fasalin takardun kudin Naira.
A halin yanzu dai kwamitin da tawagar CBN na gudanar da taro a majalisar dokokin kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsarin Sauya Fasalin Naira Zai Taimaka Wajen Dakile Magudin Zaɓe – Osibanjo
An fara taron ne da misalin karfe 12:05 na rana bayan shafe sama da awa daya ana tattaunawar sirri.
Idan dai za a iya tunawa JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa majalisar da kwamitin sun yi barazanar kama wasu da dama a ranar Alhamis bayan da Mista Emefiele ya kaurace wa gurfana a gaban majalisar dokokin.
Shugaban bankin na CBN ya sanar da tsawaita wa’adin canza kudin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu. Sai dai kwamitin ya dage cewa dole ne Emefiele ya bayyana a gabansu.
A lokacin da aka fara taron, Shugaban Kwamitin, Ado Doguwa ya ce shugaban CBN ya bayar da dalilan rashin amsa gayyatar a baya.
A wani labarin kuma,Zanga Zanga Ta Barke A Wata Jiha A Najeriya Bayan Litar Mai Ta Kai 700
Zanga-zanga ta hargitsa birnin Benin na jihar Edo, kan tashin Gwauron zabi da litar man fetur tayi zuwa naira 700.
Masu zanga-zangar dauke da alluna, suna rokon gwamnatin jihar da ta kafa kwamitin tantance farashin man fetur da sauran kayayyakin masarufi.