A yayin da wa’adin daina amfani da tsofaffin kuɗi ke ƙara gabatowa, wasu waɗanda ake zargin ƴan ta’addan ƙungiyar Islamic State of West Africa Province (ISWAP) ne sun rabawa matafiya da dama maƙudan kuɗaɗe a yankin tafkin Chadi.
Wakilin jaridar Daily Trust ya samo cewa lamarin ya auku ne ƙauyen Mairari akan babban titin hanyar Maiduguri/Monguno a ranar Asabar cikin ƙaramar hukumar Guzamala.
KU KARANTA KUMA: Rahama Sadau tayi wani muhimmin kira ga gwamnatin tarayya kan masana’antar finafinai
Wata majiya ta bayyana cewa ƴan ta’addan na ISWAP suna sanye ne da kayan sojoji sannan sun zo a manyan motoci masu ɗauke da bindigu guda biyu.
Wani mazaunin garin, Bakura Ibrahim, yace ƴan sanda sun fake ne a ƙarƙashin wata bishiya sannan suka tsaya a bakin hanya ɗauke da jakunkunan tsofaffin kuɗin.
“Mun bar Monguno da misalin ƙarfe sha biyu na rana. Yayin da muka kusa zuwa Mairari, babu jami’an tsaro ko ɗaya a wajen, hankalin mu ya fara tashi.”
“Sun tsayar damu sannan suka tambaye mu idan Maiduguri zamu je, sannan suka fara ba kowa naira dubu ɗari, lamarin ya ɗaure mana kai. Sun ba kowa da yake cikin motar ƙirar Golf Volkswagen.” A cewar Bakura.
Wata majiya ta ƙara da cewa:
“Ƴan ta’addan sun gaya mana cewa, idan kuna tunanin za ku iya zuwa bankunan su ku sauya su zuwa sababbi, ku je ku yi hakan; Allah yasa su amfane ku.”
Yadda Wata Matar Aure Ta Ƙona Kishiyarta Da Tafasashshen Ruwan Zafi
A wani labarin na daban kuma, wata matar aure ta yiwa kishiyarta ɗanyen aiki inda ta ƙonata da tafasashshen ruwan zafi.
Wata kotun majistare a birnin Ilorin ta tura wata matar aure mai suna Lola Abdulsalam, ƴar shekara 42, gidan gyaran hali bisa zargin watsawa kishiyarta Bilkisu Abdulsalam tafasashshen ruwan zafi.
Ƴan sanda a ranar Juma’a sun shigar da tuhumomi biyu akan Lola, na raunata wa da kuma ɓata suna, waɗanda suka saɓawa sashi na 247 da 292 na Penal Kod.