Wata girgizar Ƙasa mai ƙarfi data faru a yankin iyakar kasar Afghanistan a cikin dare ta hallaka mutane 920 gami da raunata wasu da dama, kamar yadda Hukumomi suka bayyana a ranar Laraba, inda ake saran za’a gina ƙasa domin gano wasu gawarwakin.
Girgizar mai ƙarfin 5.9, ta faru inda mutane suka kasance suna zaman neman ɗauki a dalilin wahalhalun da suke sha wanda karɓar Mulkin Taliban ya janyo masu a watan ogusta.
Mutuwar ta ƙaru kullum a yayin da labarin mutanen da lamarin ya shafa ya ke cigaba da shafar manyan wurare, kamar yadda Shugaban Majalisar Kolin Ƙasar Hibatullah Akhundzada, yayi gargaɗin cewa, gawarwakin zasu iya karuwa da girgizar ƙasar.
” A yanzu bayanan dake garemu yanzu shine mutane 920 sun mutu, a yayinda wasu guda 600 suka jikkata,” kamar yadda Sharafuddini Muslim, Mataimakin Ministan Kare Annoba ya sanar a taron Manema Labaru a Babban Birnin dake Kabul.