Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sallami kwamishanan lafiya, Dakta Salihu Kwayabura, daga kujerarsa.
Kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau, ya bayyana hakan a yau alata a Maiduguri, inda ya ce gwamna Zulum ya yi haka ne don gyara a ma’aikatan kiwon lafiyan jihar.
A jawabin Isa Gusau, Gwamna Zulum ya mika godiyarsa da Dr Salhiu Kwayabura bisa gudunmuwar da ya bada wajen ci gaban ma’aikatar lafiyar jihar na kimanin shekaru biyu na mukinsa.
Gusau ya kara da cewa Gwamna Zulum ya umurci shugaban ma’akatan fadar gwamnatin, Farfesa Hussain Marte, wanda shima masanin kiwon lafiya ne ya kasance kwamishinan mai rikon kwarya kafin a a nada sabo.