Gwamnatin tarayya na shirin tsawaita dakatarwar da ta yi na cire tallafin man fetur da watanni 18.
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Mista Timipre Sylva ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Sylva ya bayyana cewa gwamnati ta kammala shirye-shiryen tunkarar majalisar dokokin kasar domin yin gyara ga dokar masana’antar man fetur (PIA).